Kasar Iran Ta Sami Fasahar Kere Batira Masu Amfani Da Makamashin Nukliya
Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta shiga cikin jerin kasashe masu fasahar kere batira masu amfani da makamashin nukliya, wanda ya kaita matsayin kasa ta biyar a duniya wacce ta mallaki fasahar kere irin wadan nan batira
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Asghar Zare'an mai bawa shugaban cibiyar makamashin Nukliyar kasar shawara yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa JMI ita ce ta biyar bayan Amurka, Rasha, Faransa da kuma Britania wajen mallakar fasahar kere irin wadan nan batira.
Zare'an ya kara da cewa ana amfani da irin wadan nan batira ne a ayyukan kiwon lafiya, wato warkar da cutar kansa, komfuta, matatun man fetur da kuma canzawa taurarin dan adam wuri.
Mai bawa shugaban cibiyar makamashin nukliya ta kasar Iran ya ce hukumarsa tana kokarin hada kai da cibiyoyin ilmin nukliya a duniya don samar da batiran masu yawa don sayarwa a kasuwannin duniya.
Daga karshe Zare'an ya ce yerjejeniyar Nukliyan da kasar Iran ta cimma da manya -manayan kasashen duniya a shekara ta 2015 ya taimakawa kasar wajen ci gaba a ayyukan makamashin nukliya, harma tare da taimakon kasar Austria kasar Iran zata gina cibiyar "Ion Therapy" a lardin albus, inda an kiyasta cewa za'a kashe dalar Amurka miliyon 250 wajen gina ta.