Britania Tana Kokarin Kyautata Dangantaka Da Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i26141-britania_tana_kokarin_kyautata_dangantaka_da_iran
Gwamnatin Britania tana kokarin kyautata dangantakanta da JMI inji jaridar Guardian ta kasar a jiya Alhamis
(last modified 2018-08-22T11:31:06+00:00 )
Dec 08, 2017 12:00 UTC
  • Britania Tana Kokarin Kyautata Dangantaka Da Iran

Gwamnatin Britania tana kokarin kyautata dangantakanta da JMI inji jaridar Guardian ta kasar a jiya Alhamis

Jaridar ta kara da cewa a cikin mako mai kamawa ne ake saran sakataren harkokin wajen kasar ta Britania Boris Johnson zai ziyarci Tehran don tattaunawa kan batutuwa da dama, daga ciki har da yadda za'a yi bankunan kasar Brtania suka fara aiki a kasar ta Iran.

Labarin ya kara da cewa Britania tana bukatar bankunan kasarta su fara aiki da Iran ta tare da wani tsoro na takunkuman da Amurka ta dorawa Jumhuriyar musulunci ta Iran a wannan bangare ba. 

Kafin haka dai Boris Johnson ya je kasar Amurka don tattaunawa da majalisar dokokin kasar kan mutunta yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran amma basu fahinji juna ba. Daga bayan ne gwamnatin Amurka ta dorawa Iran da Rasha takunkuman aiki da bankunanta.