An Fara Taron Shugabanin Majalisu Na Kasashen Musulmi A Nan Birnin Tehran.
A safiyar wannan Talata ce aka fara taron shugabanin Majalisu na kasashen musulmi tare da halartar shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rauhani da Shugaban Majalisar dokokin kasar Ali Larijani a nan birnin Tehran.
Taron shi ne karo na 13 kuma ya samu halartar shugabanin Majalisu da wakilai na kasashen musulmi 41, kuma a gobe laraba ne za a kammala shi tare da fitar da bayyani na bai daya.
Kafin hakan dai, a ranakun Asabar, Lahadi da Litinin da suka gabata, kwamitoci daban daban na wannan kungiya sun gudanar da nazu zaman tare da halartar wakilai da kuma kwararru manbobi a kungiyar hadin kai na kasashen musulmi.
A yayin zaman na su kwamitin zartarwa na wannan taro, sun tattauna kan mahiman batutuwan da suka shafi siyasar kasa da kasa, kare hakin bil-adama, kare hakin mata da iyali,hakin al'adu, tattaunawa a game harakokin addinai da mazhabobi, al'amuran da suka shafi tattalin arziki da sauransu a kasashen musulmi.