Limamin Tehran:Dogaro Da Nasihohin Imam Khumain Ne Ke Kare Juyin Musulunci
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i27661-limamin_tehran_dogaro_da_nasihohin_imam_khumain_ne_ke_kare_juyin_musulunci
Ayatullah Sayyid Ali Khatami ya yi ishara da jagorancin da Imam Khomain y ayi wa juyin musulunci na Iran sannan ya ce babu yadda za a iya raba su.
(last modified 2018-08-22T07:01:20+00:00 )
Jan 26, 2018 15:43 UTC
  • Limamin Tehran:Dogaro Da Nasihohin Imam Khumain Ne Ke Kare Juyin Musulunci

Ayatullah Sayyid Ali Khatami ya yi ishara da jagorancin da Imam Khomain y ayi wa juyin musulunci na Iran sannan ya ce babu yadda za a iya raba su.

Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; A kodaushe al'ummar Iran suna cin arzikin sadaukar da kan Imam Khumain da jagorancinsa ne,kuma bisa dogaro da nasihohinsa ne juyin yake ci gaba.

Ayautullah Khamati ya kuma ce; A daidai wannan lokacin da ake bikin cika shekaru 39 da cin nasarar juyin musulunci, wajibi ne mu bayyana cewa; juyin wata ni'ima ce mai girma daga Allah ga duniyar musulunci musamman ga al'ummar Iran.

Limamin na Tehran ya bayyana Ayatullah Sayyid Ali Khamei a matsayin wanda yake ci gaba da jan ragamar juyi akan tafarkin da Imam Khumain ya shata.