Haramtacciyar Kasar Israila Ta Tabbatar Da Kawancenta Da Kasashen Larabawa Kan Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i27687-haramtacciyar_kasar_israila_ta_tabbatar_da_kawancenta_da_kasashen_larabawa_kan_iran
Priministan Haramtacciyar kasar Isara'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da kekkyawar dangantaka da mafi yawan kasashen larabawa don yakar Iran.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Jan 27, 2018 11:52 UTC
  • Haramtacciyar Kasar Israila Ta Tabbatar Da Kawancenta Da Kasashen Larabawa Kan Iran

Priministan Haramtacciyar kasar Isara'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da kekkyawar dangantaka da mafi yawan kasashen larabawa don yakar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Netanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da Talabijin ta CNN a taron tattalin arzikin da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland. 

Netanyahu ya kara da cewa dankon zumunci tsakanin kasarsa da kasashen Larabawa ya fi na shekaru 10 da suka gabata, sannan suna aikin tare don fuskantar mikiyi guda wato Iran. 

Priministan yahudawan sahyuniya ya kara jaddada cewa suna aiki kud da kud tare da kasashen Saudia da Kuma Masar don cimma manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya, da kuma hana abin da ya kira kutsawar da jamhuriyar musulunci ta Iran take yi a kasashen yankin.