Feb 02, 2018 06:02 UTC

Ranaku goma na alfijirin nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, wasu ranaku ne na tunawa da abubuwan farin ciki da sosa rai ga al'ummar Iran wanda sakamakon hadin kan al'umma da kuma jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) suka sami nasarar tabbatar da mafi girman juyin juya hali na al'umma a karni na ashirin.

Ko shakka babu samun jagoranci na kwarai da zai shiryar da kuma jagorantar duk wani juyin juya hali na al'umma zuwa ga tudun na tsirar da ake so wani lamari ne mai matukar muhimmancin gaske. A saboda haka ne juyin juya halin Musulunci na Iran karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a), wannan malami kuma masanin lamurran yau da kullum da kuma hangen nesa, ya samu nasarar kai wa ga nasara a wannan zamani na mu da babu wanda yake tunanin hakan na iya faruwa. Jagoranci na kwarai, shi ne lamari mafi muhimmanci lamarin da ya kai juyin juya halin Musulunci na Iran din ga nasara, wanda hakan kuwa ya kasance ne karkashin kulawar mutum maras  tamka irin marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda hatta a lokacin da yake gudun hijira haka ya dinga jagorancin juyin har lokacin da ya kai ga nasara a ranar 22 ga watan Bahman 1357 (11 ga watan Fabrairun 1979) kwanaki goma kacal bayan dawowarsa gida daga gudun hijira a ranar 12 ga watan Bahman (1, Fabrairu).

Alal hakika rawar da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya taka wajen samun nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, ba wani lamari ne da yake a boye ba, lamari ne da yake a fili ga kowa, wanda tsawon tarihi masana a kasashe daban-daban na duniya sun yi bahasi da kuma tabbatar da irin wannan rawar. Marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya kasance masanin irin yanayi na siyasa, al'adu da kuma zamantakewa al'ummar Iran kafin fara gwagwarmayar tabbatar da juyin da ma kuma tsakiyar lokacin da gwagwarmayar ta yi zafi, yayi amanna da cewa mafi muhimmanci dalilin nasarar wannan yunkuri na sa shi ne 'kumaji da sauyi irin na Ubangiji' wanda ya kafu cikin zukatan al'umma. Irin wannan yanayi ne ya sanya mutane daga jin kalaman marigayi Imam Khumaini (r.a) nan take suka sauya, sannan kuma cikin taimakon Ubangiji, suka zamanto babu wani tsoro da ya saura a cikin zukatansu inda cikin dukkanin jaruntaka suka fito don tinkarar gwamnatin kama karya ta Shah da kuma kifar da ita.

Bisa la'akari da muhimmancin rawar da jagoranci ya taka wajen nasarar juyin juya halin Musuluncin ne aka sanya wa ranar farko ta 'Ranaku Goma Na Alfijirin Nasarar Juyin Juya Halin Musuluncin (wato 1-11 ga watan Fabrairu) sunan ranar "Juyin juya halin Musulunci, Imam Khumaini, Wilayatul Fakih da kuma jagoranci". Ko shakka babu sanya wannan suna yana nufi da abubuwan da suka taimaka wajen nasarar juyin da kuma muhimmancin da suke da shi, wanda hakan kuma yana nuni da irin bambancin da ke akwai tsakanin juyin juya halin al'ummar Iran da sauran juyin juya halin da suka faru tsawon tarihi.

Wani lamari da yake da muhimmanci a fahimta a nan shi ne cewa muhimmancin jagorancin juyin juya halin Musulunci ba kawai ya takaita ne ga lokacin jagorantar yunkuri da mikewar al'umma don cimma manufar da aka sanya a gaba ba ne, a yanzu ma muhimmancin jagorancin yana nan daram dinsa in ma bai dara na wancan lokacin ba. A halin yanzu da ake bukukuwan shekaru 39 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci, ko shakka babu jagoranci na daga cikin abubuwa masu muhimmancin gaske da suka tabbatar da ci gaban wanzuwar juyin da kuma ci gaba da tafiyar da shi bisa ingantacciyar hanyar da ya ginu a kai tun farko. Sanya ido wajen ganin juyin juya halin Musulunci bai kauce daga tafarkin da aka gina shi a kai ba, wanda a bisa tsarin mulki da kuma mahanga ta 'Wilayatul Fakih' nauyin hakan na wuyar marigayi Imam Khumaini (r.a) a lokacin rayuwarsa, sannan a halin yanzu kuma bayan marigayi Imam Khumainin kuma a halin yanzu wannan nauyi na wuyar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne, hakan yana kara nuni da irin girman matsayi da jagorancin yake da shi ne wajen tabbatar da nasara da kuma ci gaba da dawwamar juyin juya halin Musuluncin.

Ko shakka babu 'Juyin juya halin Musulunci, Jamhuriyar Musulunci da kuma Wilayatul Fakih" wadanda marigayi Imam Khumaini (r.a) ya tafi ya bari, suna nan daram karkashin kulawar Ayatullah Khamenei, jagoran juyin juya halin Musulunci sannan kuma sun ci gaba da zama garkuwa ga kasar Iran daga makirce-makircen makiya. Don kuwa Ayatullah Khamenei ya ci gaba da riko da wannan tafarki na marigayi Imam Khumaini (r.a) wajen shiryar da juyin da kuma kiyaye koyarwarsa bugu da kari kan tsayin daka wajen tinkarar ma'abota girman kan duniya, wanda hakan ya ci gaba da samar wa juyin da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran din irin ci gaban da take ci gaba da samu wanda hatta makiyanta sun tabbatar da hakan.