Iran : Zarif Zai Halarci Taron Tsaro A Munich
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i28301-iran_zarif_zai_halarci_taron_tsaro_a_munich
A wani lokaci da yammacin yau Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawad Zarif, zai daga zuwa birnin Munich domin halartar taro kan tsaro karo na 54.
(last modified 2018-08-22T11:31:26+00:00 )
Feb 17, 2018 15:49 UTC
  • Iran : Zarif Zai Halarci Taron Tsaro A Munich

A wani lokaci da yammacin yau Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawad Zarif, zai daga zuwa birnin Munich domin halartar taro kan tsaro karo na 54.

Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Qassemi ya fitar ta ce, Muhammad Jawwad Zarif zai yi jawabi a taron gobe Lahadi, kana kuma zai yi amfani da damar domin ganawa da wasu mayan jami'ai dake halartar taron.

Sanarwar ta ce jawabinna Zarif, zai maida hankali kan batutuwan tsaro da yankin da kuma duniya.

Taron dai na kwanaki uku da aka fara jiya, na samun halartar shuwagabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin ashirin da kuma ministocin harkokin wajen da na tsaron kasashe kimanin 40. 

Makomar kungiyar tarayya Turai nan gaba, da huldar ta da kasashen Rasha da Amurka, da kuma siyasa a AFrika, da sanya ido kan makaman yaki da kuma Koriya ta Arewa na daga cikin batutuwan da taron Munich na wannan karo zai tattauna.