Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i29552-iran_ta_yi_tofin_allah_tsine_kan_gwamnatin_haramtacciyar_kasar_isra'ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi tofin Allah tsine kan kisan gillar da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka aiwatar kan al'ummar Palasdinu da suke gudanar da zanga-zangar lumana.
(last modified 2018-08-22T11:31:38+00:00 )
Apr 01, 2018 19:01 UTC
  • Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi tofin Allah tsine kan kisan gillar da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka aiwatar kan al'ummar Palasdinu da suke gudanar da zanga-zangar lumana.

A martaninsa kan harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar kan al'ummar Palasdinu da suke gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Juma'ar da ta gabata domin tunawa da cikan shekaru 42 da shelanta "Ranar Kasa" wato ranar tunawa da hakkin Palasdinawa da dawowa kasarsu da gado, Dr Ali Larijani shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi Allah wadai da haramtracciyar kasar Isra'ila tare da jaddada yin kira ga Majalisun Dokokin Kasashen Musulmi kan hanzarta daukan matakan da suka dace domin maida martani kan bakar siyasar zalunci Yahudawan Sahayoniyya.

Dr Larijani ya kara da cewa: Bakar siyasar zalunci Haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka a yankin gabas ta tsakiya zata wurga kasashen yankin cikin mummunan kangi. Kamar yadda ya fayyace matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus na Palasdinu a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa makirci ne mai tsananin hatsari da ke barazana ga zaman lafiya da sulhun yankin gabas ta tsakiya baki daya.