Limamin Juma'a: Al'ummar Iran Za Su Tsallake Wahalhanun Da Suke Gabansu
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami wanda yake yin ishara da ficewar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliya ya ce; Biyayya ga Allah madaukakin sarki hi ne hanyar warare dukkanin matsaloli
Limamin na Tehran ya kara da cewa da akwai darussa da dama da ya kamata a dauka daga lamarin wanda ya hada da cewa makiya addini ba abin dogaro ba ne.
Ayatullah Ahmad Khamati ya kuma ce; Hatta tarayyar turai ba abin dogaro ba ne kamar Amurka, domin sun ma sun karya alkawali na kin zuba hannun jari a cikin Iran.
Dangane da batun da wasu kasashen na turai suke bijirowa na makamai masu linzami na Iran, ya ce; samun waje ne ya sa suke bijiro da maganar.
Gabanin yin sallar juma'ar al'ummar Iran ta gudanar da Zanga-zanga a cikin birane da garuruwa domin yin tir da Amurka da matsayarta akan yarjejeniyar Nukliya