Iran : An Yi Zanga-Zangar Gama Gari Ta Goyon Bayan Palasdinu
Bayan gudanar da sallar Juma'a ta farko a wannan wata na Ramadana mai alfarma, al'ummar kasar Iran sun gudanar da zanga-zangar gama gari domin yin alawadai da ta'addanci da yahudawa sahayoniya ke aiwatarwa kan al'ummar Falastinu.
A rana ta biyu, kuma juma'a ta farko a watan Azumi, al'ummar kasar Iran sun gudanar da zanga-zangar yin alawadai kan dabbanci da kuma ta'addanci da jami'an tsaron HK isra'ila suka aiwatar kan al'ummar Falastinu a zagayowar ranar da aka shelanta samar da h k Isra'ila da ake kiranta da ranar Mudifa da Bala'i da kuma ranar da Amurka ta buda ofishin jakadancinta a birnin Qudus.
Mahalarta zanga-zangar sun yi ta rera taken mutuwa ga Amurka, muuwa ga Isra'ila tare kuma da yin alawadai kan ta'addancin Amurka da Isra'ila a yankin , har ila yau da kuma yadda kungiyoyin kasa da kasa suka yi shuru kan wannan ta'addanci.
Kafin hakan dai, al'ummar musulmi da 'yantattu masu son zaman lafiya a kasashe daban daban na Duniya sun gudanar da irin wannan zanga-zanga.
A ranar Litinin 14 ga watan Mayu da ta gabata, a daidai lokacin da kasar Amurka ta bude ofishin jakadancinta a birnin Qudus da kuma ta yi daidai da zagayowar ranar da aka mamaye Palastinu tare da korar Falastinawa daga kasarsu, al'ummar zirin Gaza sun gudanar da zanga-zangar nuna bakin ciki da wannan rana,inda kimanin Falastinawa 60 suka yi shahada yayin da wasu kimanin dubu uku na daban suka jikkata a lokacin da jami'an tsaron Isra'ila suka bude musu wuta.