Iran Zata Dawo Da Aikin Tace Sanadarin Uranium
Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa zata dawo da aikin tace makamashin Uranium bisa sharruddan yarjejeniyar 2015 tare da manyan kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kakakin hukumar nukliya ta kasar Iran Behrouz Kamalvandi yana fadar haka a jiya Litinin, jim kadan bayan da jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa za'a dawo da aikin tace uranium a kasar.
Kamalvandi ya kara da cewa gwamnatin Iran zata mikawa hukumar IAEA mai kula da harkokin makamashin nukliya ta duniya wasika dangane da hakan daga ofishin jakadancinta da ke Veinna .
A cikin jawabinsa na jiya a munasamar wafatin Imam Kkomaini (q) wanda ya assasa JMI, Ayatollah Khamenei jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa Iran ba zata ci gaba da mutuntuta yarjejeniyar Nukliya ta 2015 sannan kuma a gefe guda ana ci gaba da dora mata takunkumai kamar yadda wasu kasashe su ke zata ba.