Boeing Ya Soke Yarjejeniyarsa Da Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i31500-boeing_ya_soke_yarjejeniyarsa_da_iran
Kamfanin kera jiragen sama na Amurka, Boeing, ya sanar da soke yarjejeniyar da ya cimma da kamfanonin jiragen sama na Iran Air da kuma Aseman, ta tsabar kudi dalar Amurka Biliyan ashirin.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 07, 2018 01:16 UTC
  • Boeing Ya Soke Yarjejeniyarsa Da Iran

Kamfanin kera jiragen sama na Amurka, Boeing, ya sanar da soke yarjejeniyar da ya cimma da kamfanonin jiragen sama na Iran Air da kuma Aseman, ta tsabar kudi dalar Amurka Biliyan ashirin.

Kamfanin na Boeing, ya ce ya soke yarjejeniyar ce biyo jerin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, bayan janyewarta daga yarjejeniyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara 2015. 

Sanarwar da kamfanin ya fitar a jiya Laraba, ta ce yarjejeniyar da ya cimma wa da kamfanonin na Iran, da ko zasu bashi damar samar da ayyukan yi da dubban guraben ayyukan yi a Amurka.

Kawo yanzu kamfanonin na Iran basu maida martani ba kan matakin na Boieng, amma a cen baya, Jamhuriya musulinci ta Iran ta ce idan kamfanin na Boeing ya dakatar da yarjejeniyar, zai sayi wasu sabbin jiragen a wajen wasu kamfanoni.

A ranar 8 ga watan Mayu da ya gabata ne, shugaba Donald Trump, na Amurka, ya sanar da janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran, tare da mayar da duk jerin takunkuman da aka kakaba mata.