Salehi: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Za Ta Kare Manufofinta Da Dukkan Karfinta
Shugaban hukumar kula da makashin nukiliya na kasar Iran, Dakta Ali Akbar Salehi, ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta kare hakkoki da kuma manufofinta da dukkan karfinta sannan kuma ta hanya mafi kyawu.
Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana hakan ne a bayan fagen taron kasa da kasa da ake gudanar a birnin Oslo na kasar Norway da nufin tattaunawa matsaloli daban-daban da ake fuskanta a duniya inda ya ce ko shakka babu Iran za ta tsaya kyam wajen kare hakkoki da kuma manufofinta musamman dangane da batun shirinta na nukiliya.
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliyan na Iran ya kara da cewa a yayin wannan taron zai gana da babban sakataren MDD Antonio Gueterres da kuma firayi minista da kuma ministan harkokin wajen kasar Norway din don tattauna batun yarjejeniyar nukiliyan Iran da kuma ficewar da Amurka ta yi daga cikin yarjejeniyar.
Shi dai wannan taro na Oslo, wanda yake samun halartar manyan jami'an kasashen duniya daban-daban, ana gudanar da shi ne da nufin tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi tsaro da zaman lafiyar duniya don samo hanyoyin da za a bi wajen magance su.