Iran Na Goyon Bayan A Kara Yawan Danyen Man Fetur
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i31892-iran_na_goyon_bayan_a_kara_yawan_danyen_man_fetur
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC zata gudanar da taro a ranar jumma'a mai zuwa don tattauna batun kara yawan danyen man fetur a kasuwannin duniya, bisa bukatar wasu manya manyan kasashen masu sayan man a duniya wadanda suka hada da Amurka da China.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 20, 2018 18:58 UTC
  • Iran Na Goyon Bayan A Kara Yawan Danyen Man Fetur

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC zata gudanar da taro a ranar jumma'a mai zuwa don tattauna batun kara yawan danyen man fetur a kasuwannin duniya, bisa bukatar wasu manya manyan kasashen masu sayan man a duniya wadanda suka hada da Amurka da China.

Kamfanin dillancin labaran  Reuters ya nakalto Bijan Zangane ministan man fetur na kasar Iran yana kira ga kasashen da suke sayar da danyen man fiye da yawan da aka ware masu, da su dawo kan yawan da aka kayyade masu.

Minstan yana hannunka mai sanda ne ga ga kasashen Saudia da kuma wasu kasashen da basa cikin kungiyar OPEC kamar kasar Rasha da sauransu. Babban sakataren kungiyar ta OPEC Mohammad Barkindo ya bayyanawa rauters cewa yana da tabbacin cewa za'a sami fahintar juna a tsakanin kasashen kungiyar a taron ranar Jumma'a mai zuwa. 

Kasar Rasha dai tana ganin kasashen OPEC da wadanda ba sa cikin OPEC, su kara yawan man da suka haka da ganga Miliyon 1.5 don daidaita kasuwar man a duniya.

Idan haka ya tabbata, ya nuna cewa an dakatar da rage yawan man a kasuwannin duniya da ganga Miliyon 1.8 wanda kasashen suka amince da shi  watanni 18 da suka gabata don kyautata farashin man a kasuwannin duniya.

A halin yanzu dai ana saida danyen man fetur a kasuwannin duniya kan dalar Amurka $75 ko wace ganga. Kafin haka dai ana saida man kan dalar Amurka 27 kacal a shekara ta 2016.