Russia 2018 : Iran Ta Yi Kunnen Doki Da Portugal
A ci gaba da gasar cin kofin duniya da Rasha ke karbar bakunci, tawagar kwallon kafa ta Iran, ta yi kunnen doki da ta Portugal 1-1, a wasan da suka buga jiya a filin wasa na Saransk.
Wannan sakamakon dai ya sanya Iran ta yi ban kwana da gasar a kasar Rasha, inda ta samu matsayi na uku a rukunin B da take, bayan Spaniya da Portigal, wadanda suka tsallake a wasa na gaba, inda zasu fafata da Rasha da kuma Uruguay.
Har illah yau a wasannin da aka buka jiya, kasar Marocco ita ma tayi sallama da gasar bayan data yi kunnen doki da Spaniya.
Masar wacce dama tun tuni akayi waje da ita a gasar, ta kuma sha kashi a hannun Saudiyya 2-1.
Dama dai duka kasashen biyu Masar da Saudiyya sun fice daga gasar bayan da suka sha kashi a wasannin biyu na farko.
A wani wasan da ake jira yau Talata, musamman daga kasashen Afrika, shi ne wasan Najeriya da Argentina, wacce take buke bukatar ci, a yayin da Najeriya ke bukatar ko kunnen doki don tsallakawa wasan gaba, amma fa idan Croatie ta doke Iceland.