Iran Ta Yi Tir Da Yunkurin Bata Mata Suna A Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i32168-iran_ta_yi_tir_da_yunkurin_bata_mata_suna_a_faransa
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi Allah wadai da abunda ta danganta da neman bata mata suna a Faransa, bayan wargaza wani shirin kai hari kan wani taron 'yan kungiyar dake adawa da tsarin mulkin Iran a arewacin birnin Paris.
(last modified 2018-08-22T07:02:03+00:00 )
Jul 03, 2018 01:08 UTC
  • Iran Ta Yi Tir Da Yunkurin Bata Mata Suna A Faransa

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi Allah wadai da abunda ta danganta da neman bata mata suna a Faransa, bayan wargaza wani shirin kai hari kan wani taron 'yan kungiyar dake adawa da tsarin mulkin Iran a arewacin birnin Paris.

Da yake bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya ce wannan wani shiri ne kawai na neman bata wa kasarsa suna, musamman a daidai lokacinda , shugaban kasar, Hassan Rohani ya fara wata ziyarar aiki a nahiyar turai.

Mista Zarifa, ya kara da cewa, Iran kasa ce dake tir da allawadai da duk wata irin fitina da kuma ayyukan ta'addanci, a duk ko ina, kuma a shirye take da yin aiki tare da duk wadanda batun ya shafa don binciken lamarin.

A jiya ne dai hukumomin Begium, suka sanar da murkushe wani yunkurin kai hari a brinin Villepinte, dake arewacin Paris babban binrin Faransa, kan wani taron haramtacciyar kungiyar MEK ta 'yan Moudjahidine, dake yi wa tsarin mulkin Iran zagon kasa, inda aka cafke wani miji da mata 'yan kasar Belgium, amma 'yan asalin Iran dauke da wasu ababe masu fashewa, wadanda ake tuhuma don yunkurin kai harin ta'addanci.