Babu Wata Kasa Da Take Goyon Bayan Takunkumin Amurka Akan Iran
Jul 24, 2018 12:38 UTC
Dan Majalisar dattijan Amurka Chris Morphy ne ya ce; A rahoton da gwamnatin Trump ta bayar kawo ya zuwa yanzu babu wata kasa wacce ta goyi bayan Amurka na kakaba wa Iran takunkumi.
Morphy ya ci gaba da cewa; Dalili guda daya tilo da ya sa gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar Nukiliya shi ne yin matsin lamba akan Iran domin sake yin wata yarjejeniyar da Trump yake so.
Sai dai dan majalisar dattijan na Amurka ya ce; kawo ya zuwa yanzu babu wata kasa guda daya wacce ta bayyana goyon bayanta ga matakin na Amurka.
Amurka tana son dukkanin kasashen da suke sayen man fetur daga Iran da su daina baki daya, sai dai har yanzu babu daya daga cikinsu da ta aminta.
Tags