An Canza Gwamnan Babban Bakin Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i32476-an_canza_gwamnan_babban_bakin_iran
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta canza gwamnan babban bankin kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 25, 2018 11:06 UTC
  • An Canza Gwamnan Babban Bakin Iran

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta canza gwamnan babban bankin kasar.

An dai maye gurbin Valiollah Seif, dake jan ragamar babban bankin tun kama mulkin shugaba Hassan Rohani a shekara 2013, da Abdulnasser Hemmati, a cewar kamfanin dillancin labaren kasar Irna.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar, ya bukaci a kawo sauyi a harkokin bankunan da kudi, da mu'amullar bankunan kasar da sauren kasashen duniya, musamman kan harkokin canji, bayan da kudaden kasar suka rage kima sosai gaban dalar Amurka.

Duka dai wannan na daga cikin al'kawulan da gwamnatin kasar ta dauka na farfado da tattalin arzikin kasar.