Inganta Alaka da dukkanin kasashe shine babban abinda ke gaban kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i3253-inganta_alaka_da_dukkanin_kasashe_shine_babban_abinda_ke_gaban_kasar_iran
Limamin da ya jagoranci Sallar Juma'a na birnin Tehran ya bayyana cewa Inganta Alaka da dukkanin kasashe shine babban abinda ke gaban jumhoriyar musulinci ta Iran
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 11:05 UTC
  • Inganta Alaka da dukkanin kasashe shine babban abinda ke gaban kasar Iran

Limamin da ya jagoranci Sallar Juma'a na birnin Tehran ya bayyana cewa Inganta Alaka da dukkanin kasashe shine babban abinda ke gaban jumhoriyar musulinci ta Iran

A yayin da yake gabatar da hudubar juma'a, Hujatu Islam wal muslimin Kazim Siddiki ya bayyana cewa tun bayan da aka samu nasarar juyin juya halin musulinci a nan kasar Iran, magabata ke kokarin inganta alakar su tare da dukkanin kasashe Duniya face haramcecciyar kasar Isra'ila,ita kuma kasar Amurka da kanta ne ta bayyana adawarta karara da tsarin musulincin da Al'umma suka zaba da kansu, wanda hakan ya ci gaba tun daga lokacin juyin yuya halin musulincin zuwa yanzu.

Yayin da yake ishara kan yadda manyan kasashen Duniya musaman ma kasashen Turai ke bayyana adawarsu da samun 'yancin kasar Iran, Hujatul Islam Sadiki ya bayyana cewa manyan kasashen Duniyan na kokarin hana kasar Iran ci gaba a yayin da su kuma suke ta kokari wajen ci gaban kasashensu, daya daga cikin hanyoyin da suke bi shine durkusar da tattalin arzikin kasar, kuma ya kamata magabata su samar da wani muhimin sauyi a wannan bangare tattalin arziki da hakan zai tilastawa Kasashen Duniyar su yi aiki tare da kasar.a bangaren yakin tattalin arziki wajibi ne siyasar Iran ta kasance a dukkanin bangarori da suka shafi Al'adu, ilimi da kiyon Lafiya su kasance bisa tasirin siyasar juriya da kasar ke yi a bangaren tattalin Arziki.

Har ila yau Limamin da ya jagoranci Sallar Juma'a na birnin Tehran ya tabbatar da cewa wajibi ne kasar ta kara yawar karfin da take da shi a bangaren tsaro domin kare kasar daga duk wata barazanar makiya.

Daga karshe Hujjatu Islam Siddiki ya taya Al'ummar kasar murna kan zagayowar ranar jumhoriyar musulinci ta Iran da ya kama ranar 12 ga watan Farbardin wanda ya yi daidai ga 1 ga watan Avrilu , ranar da sama da kashi 98 na Al'ummar kasar suka zafi tsarin musulmci.