Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tir Da Takunkumin Amurka Akan Turkiya
A yau alhami ne ministan harkokin wajen na IRan Muhammad Jawad Zarif ya rubuta yin Allah wadai da takunkumin a shafinsa na Twitter
Muhammad Jawad Zarif ya ci gaba da cewa; Takunkumin da Amurka ta kakaba wa Turkiya wacce abokiyar kawancenta ce, yana nuni da siyasar nuna fin karfi na Amurka, sannan kuma kakaba takunkumi ya zamar mata jiki.
Baitul malin Amurka ya kakaba takunkumi akan ministan sharia na kasar Turkiya, Abdulhamid Gul da ministan harkokin cikin gida Sulaiman Soylu.
Amurka ta ce ta kakaba takunkumin ne akan mutanen biyu saboda Turkiya tana tsare da wani Baamurke kuma fasto Andrew Gulen.
Turkiya dai ta kama mutumin ne bisa samunsa da hannu a yunkurin Juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar a 2016. Har ila yau gwamnatin ta Turkiya tana zargin Andrew da alaka da Fathullah Gulen wanda aka tuhuma da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba.