Khudubar Jumma'a: Gwamnatin Iran Ba Za Ta Tattauna Da Amurka Ba
Na'ibin limamin masallacin jumma'a a nan Tehran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran da shugaban kasar ba zasu sake shiga tattaunawa da gwamnatin Amurka ta yanzu ba.
Hujjatul Islam Kazim Sadiqi ya bayyana haka ne a khudubobinsa ta sallar jumma'a a nan Tehran, ya kuma kara da cewa ficewar gwamnatin Amurka daga yerjejeniyar shirin nikliyar kasar Iran a cikin watan Mayun da ya gabata ya rufe duk wata kofa ta tattunawa da ita.
A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tattaunawa da kasar Iran ba tare da wani sharadi ba.
Har'ila yau Hujjatul Islami Sadiqi ya yi maganar ranar kare hakkin bil'adama a musulunci, wanda ita ce ranar 5 ga watan Augusta na ko wace shekara. Na'ibin limamin ya kara da cewa musulunci yana da hakkin bil'adama na gaskiya kuma shi ne ya ke kare hakkin bil'adama da gaskiya.
Daga karshe limamin ya yi maganar nasarorin da ake samu a kan yan ta'adda a kasashen Siriya da Yemen, inda ya bayyana cewa wannan alama ce ta karshen yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya.