Iran : An Bude Taron Kasa Da Kasa kan Hakkin Bil'adama A Musulunci
A safiyar yau Asabar ne aka bude taron kasa da kasa kan hakkin bil'adama a musulunci karo na ukku a nan Tehran.
Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa malamai da masana da dama daga kasashen duniya daban daban ne suka samihalattan taron. Labarin ya kara da cewa Atiyyatu Qashuni shugaban cibiyar kare hakkin mata a nan Iran, a jawabinta na bude taron dazo dazun nan a nan Tehran ta bukaci musulmi am duniya su yi kokarin ganin hakkin bil'adama a musulunci ya sami tafiya da kafafunsa a cikin al'ummar musulmi.
Wakilan kungiyoyi da cibiyon addinin musulunci, daga ciki har da na kasar Yemen suka sami halattan taron na hakkokin bil'adama a musulunci.
Ranar biyar ga watan Augusta na ko wace shekara, wato 14 ga watan Murdod a calandar Iraniyawa ita ce ranar hakkin bil'adama a musulunci.