Majalisar Dokokin Kasar Iran Ta Tube Ministan Kwadago Daga Mukaminsa
Aug 08, 2018 11:56 UTC
Majalisar dokokin kasar Iran ta tube ministan gwadago da kamfanono Ali Rabiei daga mukaminsa bayan ya kasa gamsar da su dangane da yadda lamuran tattalin narzikin kasar suka lalace a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a safiyar yau Laraba ne ministan ya je gaban majalisar don kare kansa a kan korafe korafen majalisan kan yadda yake tafiyar da ma'aikatarsa. musamman ganin yadda kudaden kasar Rial suka fadu da kashi kimani 80% idan kan kwatantan da dalar Amurka.
Labarin ya kara da cewa yan majalisa 129 suka bukaci a tsige ministan a yayinsa da 111 suka goyi bayansa sannan wasu 3 suka ki kada kiri'insu.
Tags