Macron: Tarayyar Turai Tana Son Kare Yarjejeniyar Nukiliya
(last modified Tue, 28 Aug 2018 07:22:35 GMT )
Aug 28, 2018 07:22 UTC
  • Macron: Tarayyar Turai Tana Son Kare Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban kasar Faransa ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da jakadun kasar a birnin Paris a jiya litinin

Emmanuel Macron ya kuma yi suka akan matsayar Amurka dangane da batutuwa daban-daban da su ka hada da ficewarta daga cikin yarjejeniyar Nukiliya sannan ya jaddada cewa; Faransa za ta kare yarjejeniyar Nukiliya

Donald Trump shugaban kasar Amurka ya sanar da ficewar kasarsa daga yarjejeniyar ta Nukiliya ne a ranar 8 ga watan Mayu. Kasashe da dama sun yi tir da matakin na shugaban kasar Amurka, tare da yin kira da a kare yarjejeniyar

Kasashen Faransa, Birtaniya, SIn, Rasha, Jamus da kuma tarayyar turai suna daga cikin masu kokarin ganin yarjejeniyar ba ta rushe ba.

Tarayyar Turai ta yi alkawalin bayar da dukkanin taimakon da za ta iya domin kare yarjejeniyar.