Iran Na Zargin Saudiya Da Maida Kungiyar OPEC Kayan Aiki Ga Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i33209-iran_na_zargin_saudiya_da_maida_kungiyar_opec_kayan_aiki_ga_amurka
Jakadan kasar Iran a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ya zargi kasashen Saudiya da Hadaddiyar daular larabawa da maida kungiyar a matsakin kayan aiki ga Amurka.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Sep 16, 2018 14:34 UTC
  • Iran Na Zargin Saudiya Da Maida Kungiyar OPEC Kayan Aiki Ga Amurka

Jakadan kasar Iran a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ya zargi kasashen Saudiya da Hadaddiyar daular larabawa da maida kungiyar a matsakin kayan aiki ga Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hossein Kazempour Ardebili, yana fadar haka, ya kuma kara da cewa yerjejeniya tsakanin kasashe masu arzikin man fetur mambobi a kungiyar da kuma wadanda suke wajen kungiyar na tsakaita yawan man fetur da ko wace kasa ke haka ya taimaka wajen daidata farshin man fetur a duniya, amma a halin yanzun da Amurka tana son hana kasar Iran saida danyen man fetur da take haka a kasuwannin duniya tuni kasashe kamar saudia da hadaddiyar daular larabawa da Rasha da kuma Najeriya sun kara yawan man fetur da suke haka don cike gurbin ganga miliyon 2.5 wanda Iran take haka kafin takunkumin ya kamkama a nan gaba. 

 Hossein Kazempour Ardebili, ya ce tuni wadanda kasashe sun amince da takunkumin zaluncin da Amurka ta dorawa daya daga cikin mambobin kungiyar harma suna kokarin cike gibin da ficewar iran zai jawo a kasuwan man fetur a duniya.