Rouhani: Iran A Shirye Take Ta Tinkari Amurka Da 'Yan Amshin Shatanta
(last modified Sun, 23 Sep 2018 17:44:34 GMT )
Sep 23, 2018 17:44 UTC
  • Rouhani: Iran A Shirye Take Ta Tinkari Amurka Da 'Yan Amshin Shatanta

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Amurka tare da daukin wasu kananan kasashe 'yan amshin shatanta suna kokari ne wajen haifar da yanayin rashin tsaro a Iran, to amma Jamhuriyar Musulunci a shirye take ta tinkare su.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a yau din na Lahadi jim kadan kafin ya tashi zuwa birnin New York don halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda yayin da yake magana dangane da harin ta'addancin da aka kai garin Ahwaz da ke kudu maso yammacin kasar ta Iran da yayi sanadiyyar shahadar mutane 25 inda ya ce: Amurkawa suna son dagula yanayin tsaro ne a kasar Iran. Suna son haifar da zaman dardar da rashin tabbas don su sami damar dawo da ikonsu a kasar nan, to amma babu guda daga cikin hakan da zai faru.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Al'ummar Iran ba za su taba amincewa da hakan ba, sannan kuma gwamnatin Iran ma ta shirya kanta wajen tinkarar wannan bakar aniya ta Amurkan. Ko shakka babu Amurkawa za su yi nadamar wannan abin da suka aikata, don kuwa sun ba su canka daidai ba.

Shugaba Rouhani ya ce Amurka ita ce take sanya wasu kasashen larabawan yankin Gabas ta tsakiya suke adawa da Iran, yana mai cewa a fili yake mun san wadanda suke da hannu cikin wannan hari na ta'addanci da kuma wadanda suke wa aiki. Don haka ya ce ko shakka babu Amurka ba za ta cimma wannan mafarki da take yi na cimma manufofinta a kan Iran ba.