Larijani: Amurka Da Isra'ila Su Ne Ummul Aba'isin Rashin Tsaro A Duniya
Kakakin majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran, Dakta Ali Larijani ya bayyana cewar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila su ne ummul aba'isin din dukkanin rashin tsaron da ake fuskanta a duniya.
Dakta Larijani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen taron shugabannin majalisun kasashen Turai da Asiya da ake gudanarwa a birnin Antalya na kasar Turkiyya inda ya ce matsaloli da rikice-rikicen da ke faruwa a duniya a halin yanzu sun samo asali ne sakamakon irin siyasar Amurka da HKI don haka yayi kira ga kasashen duniya da su hada kansu waje guda.
Dakta Larijani ya ce siyasar son kai da neman mulkin mallaka na Amurka su ne suka haifar da matsaloli da dama da duniya take fuskanta, yana mai kiran Amurkan da ta sake yin dubi cikin siyasar nata.
A jiya Talata ce dai aka bude wannan taron da ya sami halartar shugabannin majalisun kasashe daban daban.