Iran : Jagora Ya Jaddada Wajabcin Bunkasa Harkar Ilimi
(last modified Wed, 17 Oct 2018 18:57:25 GMT )
Oct 17, 2018 18:57 UTC
  • Iran : Jagora Ya Jaddada Wajabcin Bunkasa Harkar Ilimi

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya jaddada wajabcin daukan matakan bunkasa harkokin ilimi a kasar Iran tare da yin watsi da farafagandar makiya.

A ganawarsa da tawagar masana harkar ilimin kimiyya musamman matasa daga cikinsu a yau Laraba: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khameine'i ya jaddada daukan matakan bunkasa harkokin ilimi a Iran tare da yin watsi da duk wata farafagandar makiya ta kokarin nesanta al'ummar Iran daga fannonin ilimi musamman makircin da suke kullawa na aiwatar da kashe-kashen gilla kan masana da manazarta da nufin raunana harkar ilimi a cikin kasar ta Iran.

Jagoran ya kara da bayyana cewa: Makiya suna kokarin bata sunan kasar Iran tare da raunana gwiwar al'ummarta a kokarin da suke yi na bunkasa harkar ilimi a bangarori da dama, amma wannan makirci nasu ba zai taba cimma nasara ba.

Har ila yau Ayatullahi Khameine'i ya jaddada wajabcin musayar ilimi da fasaha a tsakanin kasashe da kuma tsakanin masana da nufin bunkasa harkar ilimi a tsakanin jinsin bil-Adama. Yana mai fayyace gagarumar tasirin da ilimi ke yi a fagen rayuwar bil-Adama.