Sabon Takunkumin Amurka Kan Iran Ya Fara Aiki A Yau
(last modified Mon, 05 Nov 2018 06:21:10 GMT )
Nov 05, 2018 06:21 UTC
  • Sabon Takunkumin Amurka Kan Iran Ya Fara Aiki A Yau

A yau ne sabon takunkumin Amurka ke fara aiki a kan kasar Iran, wanda zai shafi bangaren sayar da man fetur da sauran lamurra da suka shafi makamashi na kasar.

Takunkumin na Amurka dai na zuwa ne 'yan watanni bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran da sauran manyan kasashen duniya.

Babu wata kasa daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya da ta amince da wannan mataki da Amurka ta dauka.

A nata bangaren kasar Iran ta bayyana matakin na Amurka da cewa ya kara fito da matsayin gwamnatin Amurka a fili ne, kan cewa ita ce take karya ka'idoji da yarjeniyoyi na kasa da kasa.

Iran dai ta ce za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniyar matukar dai sauran bangarorin da suke cikin yarjejeniyar suna ci gaba da mutunta ta, ko da kuwa ba tare da Amurka ba.