Hukumar Sadarwa Tsakanin Bankuna SWIFT Ta Yanke Hulda Da Bankunan Iran
(last modified Thu, 08 Nov 2018 06:41:59 GMT )
Nov 08, 2018 06:41 UTC
  • Hukumar Sadarwa Tsakanin Bankuna SWIFT Ta Yanke Hulda Da Bankunan Iran

Hukumar sadarwa tsakanin bankuna a duniya SWIFT ta bada sanarwan dakatar da hulda da bankuna kasar Iran

SWIFT wacce take da mazauni a kasar Belgium ta bada wannan sanarwan ne a ranar Litinin, ta kuma kara da cewa ta dau wannan matakin ne don biyayya ga gwamnatin Amurka wacce ta sake maida takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa Iran kan shirinta na makamashin Nukliya.

Labarin ya kara da cewa wannan haramcin zai shafi bankunan kasar Iran 50 da rassansu a duk fadin kasar. Hukumar SWIFT dai ita ce hukuma mai sadarwa tsakanin bankuna da cibiyoyin kudade kimani 11,000 daga kasashen kimani 200 a duniya.

Khidimar da hukumar SWIFT ta ke yi sun hada da sawwaka huldar kasuwanci da hada-hadar kudade tsakanin kamfanoni, gwamnatoci, cibiyoyin kudade da kuma yan kasuwa a duk fadin  duniya. 

A shekara ta 2015 ne aka daukewa kasar Iran wani bangare na takunkumin aiki da hukumar SWIFT bayan ta cimma yerjejeniya kan shirinta na makamashun Nukliya da manya manyan kasashen duniya 51. Amma gwamnatin Shugaban Trump na Amurka, da farko ta fice daga yerjejeniyan sannan ta sake maida takunkuman aka daukewa kasar ta Iran,  don tilasta mata sake kulla wata sabuwar yerjejeniya.

Sai dai gwamnatin kasar Iran,  ta bayyana cewa tana aiki tare da sauran kasashen da suka ci gaba da mutunta yerjejeniyat ta shekara 2015, musamman kasashen tarayyar turai don samar da wata kafa ta hada-hadar kudade da kasuwanci a tsakaninsu da Iran da kuma sauran kasashen duniya.