Rauhani: Al'ummar Iran Za Su Yi Tsayin Daka Wajen Fuskantar Takunkumin Amurka
(last modified Sat, 10 Nov 2018 19:02:16 GMT )
Nov 10, 2018 19:02 UTC
  • Rauhani: Al'ummar Iran Za Su Yi Tsayin Daka Wajen Fuskantar Takunkumin Amurka

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya ce; al'ummar Iran za su ci gaba da yin tsayin daka wajen fuskantar takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasarsu.

Rauhani ya bayyana hakan ne yau a lokacin wani zama da aka gudanar tsakanin bangarorin zartarwa, dokoki da kuma shari’a a yau a birnin Tehran.

Shugaban ya ce takunkumin Amurka ba zai iya hana Iran fitar da mai ko sayar da shi a duniya ba, domin kuwa Iran tana da hanyoyi daban-daban da za ta iya kare harkokin cinikayyar mai da take hakowa.

Rauhani ya kirayi al’ummar kasar ta Iran da su gaba da kare hadin kan da ke tsakaninsu, da kuma kara bayar da himma tukuru wajen karfafa ayyukansu da kere-kerensu, da sauran bangarorin ayyukan ilimi da aka san su da bada kwazo a kansu, ta yadda hakan zai zama babbar amsa ga takunkumin na Amurka.

Dukkanin kasashen duniya da suke yin mu'amala da Iran sun yi watsi da wannan takunkumi na Amurka a kan Iran, musamman ma wadanda suke sayen danyen mai daga kasar ta Iran, wanda ala tilas Amurka ta dawo ta lashe amnta da cewa, ta yi afuwa ga kasashe 8 da suke sayen mai daga Iran da su ci gaba da, wanda masana da dama suke kallon hakan a matsayin gazawa daga Amurka.