An Fallasa Wani Makircin Da Gwamnatin Saudia Ta Kullawa Iran
Jaridar New York Time ta kasar Amurka ta nakaltu majiyar jami'an tsoro kusa da yerima mai jiran gadon kasar Saudiya dangane da shirin kashe biliyoyin dalar Amurka don rikita kasar Iran.
Jaridar New York Times ta nakalto Ahmad Asiri tsohon kakakin sojojin kawancen masu yaki da gwamnatin kasar Yemen yana fadawa George Nader wani dan kasuwa dan kasar Lebanon kuma na kusa da fadar shugaban kasar Amurka, da kuma Joel Zamel wani dansandan ciki na HKI kan cewa gwamnatin kasar Saudia ta ware dalar Amurka billiyon biyu don wargaza tsarin tattalin arzikin kasar Iran da kuma kashe manya manyan jami'an gwamnatin kasar.
Jaridar ta kara da cewa George Nader ya bukaci Saudia ta yi amfani da wani kamfanin na kasar Britania don aiwatar da wannan shirin.
Kisan da gwamnatin saudia ta yi wa Jamal Khashaggi dan jarida mai rubutu a jaridar Washington Post ya sa kafafen yada labarai musamman jaridu suka fara neman wasu matsalolin gwamnatin ta Saudia suna fallasasu.