Iran Ta Yi Allawadai Harin Isra’ila Kan Tashar Al-aqsa
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qasemi ya bayyana harin Da Isra’ila ta kai kan ginin tashar talabijin ta al-aqsa da cewa aiki ne na ta’addanci.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qasemi ya bayyana harin Isra’ila kan ginin tashar talabijin ta al-aqsa da ke Gaza da cewa aiki ne da ya cancanci Allawadai.
Yace ko shakka babu Isra’ila bata taba boye manufarta wajen yaki da duk wani alami na addini ko zamantakewa ko wani abu mai alaka da rayuwar al’umma da jin dadinsu ba, inda takan kai hare-haren dabbanci a kan komai.
Qasemi ya kirayi sauran kasashen duniya da su sauke nauyin da ke kansu na takawa Isra’ila burki kan kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Palastine tsawon fiye da shekaru 70 da suka gabata har zuwa yau.