Iran Ta Danganta Takunkuman Amurka A Matsayin Ta'addanci Kan Tattalin Arziki
(last modified Mon, 10 Dec 2018 11:23:24 GMT )
Dec 10, 2018 11:23 UTC
  • Iran Ta Danganta Takunkuman Amurka A Matsayin Ta'addanci Kan Tattalin Arziki

Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran, Dakta Hassan Rouhani, ya soki matakan Amurka na kakaba wa kasarsa takunkumi, yana mai bayyana yunkurin a matsayin ta'addanci kan tattalin arziki.

Yayin taron kasa da kasa kan kalubalen ta'addanci, Shugaba Rouhanin ya yi bayanin cewa, ta'addanci kan tattalin arziki na nufin haifar da fargaba game da tattalin arzikin wata kasa tare da hana sauran kasashe zuba jari da aiwatar da cinikayya da ita.

Ya ce janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran tare da mayar da takunkumai kan kasar da matsawa abokan cinikayyarta lamba, babban misali ne na ta'addanci kan tattalin arziki.

Taron wanda aka kaddamar a ranar Asabar data gabata a nan Tehran, ya samu halartar wakilai daga kasashen Afghanistan da Sin da Pakistan da Rasha da kuma Turkiyya.