Aya. Larijani Ya Zama Shugaban Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Mulki Na Iran
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khamina'i ya nada Aya. Amuli Larijani a matsayin sabon shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin mulki a nan Iran.
Kamfanin dillancin labaran Irna a nan Iran ya nakalto ofishin jagoran juyin juya halin yana bada wannan sanarwan a shafinsa na yanar gizo a yau Lahadi.
Jagoran ya bayyana muhimmancin majalisar fayyace maslahar tsarin mulki a harkokin gudanarwa a gwamnatin JMI a nan Iran, ya kuma kara da cewa, bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar Aya. Hashimi Sharudi a makon da ya gabata ya ga Aya. Sadid Amuli Larijani ya cancanci jagorantar wannan majalisar don irin korewan da yake da shi a harkokin shari'a da kuma na gudanarwa.
Banda haka a cikin sanarwan Jagoran ya sanya Aya. Sadiq Amuli Larijani a cikin majalisar kare kundin tasarin mulki na JMI. Kafin haka dai Aya. Sadiq Amuli Larijani shi ne Alkalin alkalai na Jumhuriyar musulunci ta Iran.