Iraniyawa Sun Fito Tattakin Nuna Goyon Baya Ga Tsarin Musulunci
Miliyoyin Iraniyawa sun fito tattaki na tunawa da tattakin 9 ga watan Day na kalandar Iraniyawa a shekara ta 2009 don kawo karsfin fitina.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa miliyoyin Iraniyawa a lardunan kasar suka fito yau lahadi 9a ga watan Day don tunawa da basiran da suka yi na kawo karshen fitanan da ta auku bayan zaben da aka gudanar a farkon shekara ta 2009.
Yan takarar shugaban kasa Karubi da kuma Mir Husain Musawi ne suka ingiza fitana bayan zaben inda suka yi korafin cewa an yi masu magudi amma kuma sun ki bin hanyoyin da suka dace na gabatar da korafinsu.
Kasashen yamma sun yi amfani da fitinan inda wasu yan koren kasashen suka tayar bayan zaben don cimma manufofinsu na ganin bayan gwamnatin JMI.
A lokacin dai fitowar miliyoyin Iraniyawa a duk fadin kasar suna jaddada goyon bayansu ga tsarin JMI sannan suna Allah wadai da masu fitana ya taimakwa wajen dawo da zaman lafiya a kasar.
A Jawabin da ya gabatar a karshen tattaki na yau a dandalin Imam Husain (a) da ke nan Tehran. Mataimakin babban komandan dakarun juyin juya halin musulunci , Brigadier General Hossein Salami, ya ce fitinan shekara ta 2009 ya fi zama hatsari ga JMI a kan kallafeffen yaki na shekaru 8 da kasar Iraqi.
Daga karshe Brigadier General Hossein Salami ya bukaci mutanen kasar Iran su ci gaba da sanya ido a kan makiya da kuma makircemakircensu.
I