Iran Zata Kara Dankon Zumunci Da Maurintania
Jakadan kasar Iran a kasar Mauritania yan gana da Firai Ministan kasar A Ranar Alhamis da ta gabata inda suka tattauna batun karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
kamfanin dillancin labaran Iran na kasar Iran ya bayyana cewa jakadan Muhammad Umrani ya gana da Firai minista Muhammad Salam Albashir ne a birnin Nuwakhshot babban birnin kasar ta Morocco a ranar Alhamis da ta gabata inda ya bayyana masa shirin JMI na kara fadada dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Firai ministan a nashi nbangaren ya bayyana cewa gwamnatinsa tana bukatar fadada dangantaka da kasar iran a bangarorin makamshi mai fetut da samar da ruwa da kuma ma'adinai.
Kafin haka dai jakadan kasar na Iran ya gana da shuagaban jam'iyya mai mulkin kasar ta Mauritaniya Muhammad Alhatam inda suka tattauna batutuwa da dama, wadanda suka hada da karafafa dangantakar al-adu da da kasuwanci tsakanin kasashen biyu.