Iran Ta Ja Kunnen Poland, Game Da Taron Amurka A Kasar
Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta Iran ta kira jami'in kula da harkokin waje na kasar Poland, dake birninTehran, domin nuna masa matukar bacin ranta dangane da wani taro na kyammar Iran din, da Amurka ke shirin gudanarwa a kasar ta Poland.
Iran dai tana mai nuna bacin ran ta ne kan taron da Amurka ke shirin gudanarwa kan Iran a watan gobe a kasar ta Poland wanda ta ce na nuna kiyaye ne gare ta, wanda kuma a cewar Iran zai iya dagula alakar dake tsakanin kasashen na Iran da Poland.
Da yake fayace manufar taron, Jami'in kasar ta Poland, Wojciech Unolt, ya bayyana cewa akwai sabani tsakanin kasarsa da Amurka dangane da manufar taron, saidai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce bata kai ga gamsuwa ba da bayannin da jami'an ya yi ba, kuma zata iya daukar mataki muddin aka samu akasin hakan.
A ranar Juma'a data gabata ce, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sanar cewa za'a gudanar da wani taro kan tsaro a yankin gabas ta tsakiya, wanda a cewarsa babban manufarsa shi ne karya laggon Iran a yankin.
Kan hakkan dai 'yan majalisar dokokin Iran da dama suka bukaci da kori jakadan na Poland a Iran, a matsayin maida martani.
Ko baya ga hakan ma a wani mataki na maida martani ga kasar ta Poland, kungiyar 'yan fina finai Sinima ta Iran, ta soke wani bikin baje kolin fina-finan Poland da aka shirya gudanarwa a watan gobe a birnin Tehran.
A nasa bangare kuwa ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, tini ya yi ga mahukuntan kasar ta Poland dangane da sadaukarwar da Iran ta yi wa kasar ta Poland a yayin yakin duniya na biyu, lokacin da ta karbi 'yan gudun hijira dubu dari (100,000) na kasar ta Poland.