Iran : Zarif, Ya Bukaci Amurka Ta Gaggauta Sakin 'Yar Jadidar PRESSTV
(last modified Thu, 17 Jan 2019 04:38:57 GMT )
Jan 17, 2019 04:38 UTC
  • Iran : Zarif, Ya Bukaci Amurka Ta Gaggauta Sakin 'Yar Jadidar PRESSTV

Ministan harkokin wajen Jamhuriya Muslinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bukaci Amurka data gaggauta sakin 'yar jaridar nan ma'aikaciyar tashar talabijin ta kasa da kasa mallakin Iran, PRESSTV, cewa da Mardiyat Hashimi da hukumar leken asiri ta kasar FBI ke tsare da.

A wata hira da gidan talabijin na kasar Al-Alam TV,  Mista Zarif ya bayyana kamun 'yar jaridar da batun siyasa wanda ba za'a amince dashi ba, tare da bayyana hakan a matsayin toye 'yancin fadar albarkacin baki.

Mista Zarif, ya kara da cewa, ''tun bayan aurenta da ba'iraniye, Mme Hashimi, tana a matsayin 'yar Iran, a don haka yauni ne a wuyanmu mu kare hakkin 'yan kasarmu''. 

‘Yar jaridar Mardiyat Hashimi, wacce ‘yar asalin kasar Amurka ce, ta tafi Amurkan ne don ziyartar dan uwanta wanda bashi da lafiya da kuma sauran danginta, inda jami’an tsaron suka kama ta a filin jirgin sama na kasa da kasa na St. Louis dake jihar (Missouri) a ranar Lahadi, daga nan kuma aka mika ta ga jami’an hukumar FBI, wadanda suke tsare da ita a birnin Washigton.

Dama kafin hakan ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran cikin wata sanarwa data fitar ta yi tir da allawadai da kame 'yar jaridar, tare da bukatar a sallame ta ba tare da wata wata ba.

Haka ma a cikin wata sanarwa da kungiyar 'yan jarida ta Iran, ta fitar, ta caccaki Amurka, dangane da kame 'yar jaridar ta PRESSTV, Mardiyah Hashemi, a daidai lokacin da Amurkar take buga gaba da cewa ita ce misali na kare hakkin bil adama.

Kungiyar ta kara da cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da 'yan jaridan na Iran ke fuskantar cin zarafi daga gwamnatin Amurka ba.