MDD Ta Nuna Damuwarta Da Takunkuman Da Amurka Ta Dorawa Iran
Shugaban ofishin jakadancin MDD a birnin Tehran ya bayyana damuwar MDD da takunkuman da Amurka ta dorawa JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Maria Dotsenko jakadan MDD a Tehran yana fadar haka a safiyar yau Litinin ya kuma kara da cewa dukka rahotannin hukumar IAEA mau kula da lamuran Nukliya a duniya sun tabbatar da cewa kasar Iran bata sabawa alkawuran da ta dauka a yerjejeniyar da ta kulla da kasashen 5+1 a shekara ta 2015 ba.
Dotsenko ya kara da cewa saboda haka ne ma sauran kasashen da suka kulla wannan yerjejeniyar suke ci gaba da mutunta yarjejeniyar.
A wani bagare kuma jakadan MDD a nan Tehran ya ce MDD tana allawadai da kungiyoyin yan ta'adda wadanda suke kashe mutane a nan kasar Iran .
Kungiyar yan ta'adda ta MKO ta munafukai makiya JMI dai suna ci gaba da samun tallafin wasu kasashen Turai. MKO ta kashe mutane kimanu dubu 17 a JMI tun bayan samuwarta.