An Saki 'Yar Jaridar Press Tv Marzieh Hashemi
Shugaban hukumar gidan Radio da Talabijin dake watsa shirye-shiryenta na bangaren kasashen waje na kasar Iran ya yi murna da sakin da aka yiwa Marzieh Hashemi 'yar jaridar tashar talabijin na Press Tv, sannan ya tabbatar da cewa tilastawar da Al'ummar Duniya ta yi wa gwamnatin Amurka shi ya sanya ta sako 'yar jaridar.
Jabali ya tabbattar da cewa akwai bukatar kara fadakarwa da kuma bayyanawa mutane abinda ke faruwa a Duniya musaman ma mutanan Amurka ta yadda za su kara tilastawa gwamnatinsu ta sako mutanan da take riko da su ba tare da sun aikata wani laifi ba.
Jabali ya kara da cewa sakin Uwar gida Hashemi babbar nasara ce ga kafafen yada labarai masu 'yanci musaman ma tashoshin talabijin na Press Tv da Al-alam mallakin jamhoriyar musulinci ta Iran.
A marecen jiya Laraba ne aka sako Marzieh Hashemi 'yar jaridar tashar talabijin na Press Tv ta nan kasar Iran a birnin Washington, bayan ta kwashe kwanaki 11 a gidan Kaso ba tare da an tuhume ta da wani laifi ba.
A ranar 13 ga watan janairu ne aka kama Marzieh Hashemi 'yar asalin kasar Amurka da take aiki jarida a tashar talabijin din Press Tv dake nan birnin Tehran, a filin jirgin ST.Louis, sannan aka isa da ita zuwa wani ofishin 'yan sanda na FBI dake birnin Washington.
Marzieh ta je kasar ta asali ne domin ganawa da iyalai da 'yan uwanta, a yayin da aka kamata ta fuskanci cin mutunci da wulakanci daga jami'an tsaron na Amurka, tun da cewa sun musulma ce amma sun cire mata hijabi kuma sun tilastamata ciin abinci da ya haramta ci a addinin musulinci.