Iran Ta Yaye Labulen Wani Sabon Makamin Mai Linzami
(last modified Sat, 02 Feb 2019 11:54:51 GMT )
Feb 02, 2019 11:54 UTC
  • Iran Ta Yaye Labulen Wani Sabon Makamin Mai Linzami

Kwararru a ma'aikatar tsaron kasar Iran sun sami nasara kera wani sabon makamai mai linzami mai cin dogon zango.

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta bayyana cewa an baje kolin wannan makamin a baje kolin ci gaba a bangaren tsaron da JMI ta samu a bikin cika shekaru 40 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. 

A bukin yaye labulen wanan makamin mai suna HAWIZEH Brigadier General Amir Hatami ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa makamin zai sami bararsa mai nisan kilomita 1350 ba tare da kuskure masa ba. Kuma yana karfin yin barna idan ya fada kan bararsa. 

Hatami ya kara da cewa JMI ba zata taba shiga tattaunawa da wata kasa kan shirinta na makamai masu linzami ba. Ya kuma kammala da cewa dukkan makaman da ma'aikatar tsaron kasar take kerawa don kariya ne ba da nufin kuttatawa wata kasa ba.

A nashi bangaren Shugaban dakarun juyin juya halin musulunci Amir-Ali Hajzadeh ya bayyana cewa JMI tana da fasahar kera ko wani irin makami mai linzami da taga dama bayan da ci karfin matsalolin kera ingin jragen yaki a baya.

A shekarar da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana ficewarsa kasarsa daga yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran saboda rashin hada makamai masu linzami a cikin abubuwan da aka hana iran samar da su a cikin yerjejeniyar.