Sharhi:Suka Ta Siyasa A Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Ba Laifi Bane
(last modified Wed, 06 Feb 2019 06:48:32 GMT )
Feb 06, 2019 06:48 UTC
  • Sharhi:Suka Ta Siyasa A Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Ba Laifi Bane

Alkalin alkalan JMI Aya. Sadiq Larijani Ya bada sanarwan cewa an yi afwa ga fursinoni masu yawa a dai-dai lokacin da kasar take cika shekaru 40 da juyin juya halin musulunci a kasar.

A ranar litinin da ta gabata ce alkalin alkalan JMI ya bada sanarwan cewa ya bukaci jagoran juyin juya halin musulunci a kasar ya yi afwa ga dimbin fursinoni a da-dai lokacinda ake bukukuwan cika shekaru 40 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, inda jagoran ya amince da dukkan bukatun da ya neman. 

Ammam Aya. Larijani ba kara da cewa , abin mamake shi ne wasu suka fara bayyana ra'ayinsu kan cewa yakamata wannan afwar ta shafi wadanda suke kira fursinonin siyasa. Larajini ya kara da cewa a nan Iran bawa da wani fursina wanda ake kira fursinan siyasa. 

Alkalin alkalan wannan afwa da jagoran juyin juya halin musulunci ya amince da shi ya shafi fursinonin kimani dubu 50 ne, kuma an yi shi ne don tausayi da jinkai ga wadanda suke cikin wannan halin ne, duk wani wanda zai bada wata fassara ga wannan aikin yayi babban kuskure.

Ya ce tsarin JMI yana da dokokin isassu a ko wani bangaren, don haka yakamata masu irin wannan maganan su san cewa akwai bambanci tsakanin Karayi, da wulakanci da kuma suka a cikin kundin tsarin mulki na JMI. Don haka a fila nake nanatawa kan cewa suka a JMI ba laifi bani. Wannan kuma ya hada har ga shugaba mafi girma a kasar.

Sai dai yakamata a bambanta tsakanin sukan ra'ayin wani dan siyasa da kuma wulakanta tsarin musulunci wanda yake jagorancin kasar wanda kuma sai da mutane suka gudanar da zaben raba gardama wanda ake kira referandom, tare da samun amincew mafi koli na kashe 98.2% kafin kafa tsarin. 

Manufar wadanda suke irin wadannan maganganu shi ne nun acewa akwai fursinonin siyasa a JMI a daya bangaren sannan a wani bangaren kuma sunan son nuna cewa tsarin musulunci a nan JMI baya yarda da suka, wanda haka ba gaskiya bane. 

Daga karshe alkalin alkalan ya bayyana cewa ma'aikatar shari'a bata taba kama wani da sunan wai yana sukar hukumar JMI ta Iram ba.