Iran Na Bikin Cika Shekaru 40 Cif Da Nasarar Juyin Musulunci
(last modified Mon, 11 Feb 2019 04:31:23 GMT )
Feb 11, 2019 04:31 UTC
  • Iran Na Bikin Cika Shekaru 40 Cif Da Nasarar Juyin Musulunci

Yau, 11 ga watan Fabarairu, al'ummar Iran ke bikin cikar shekaru 40 cif da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda aka samar a rana irinta yau ta 1979 karkashin Jagorancin marigayi Ayatollah Iman Khomeini.

Bikin na bana dai ya sha bamban dana sauren shekaru, duba da iya shekarun da kasar ta kwashe kan wannan turba, duk da barazanar da take fuskanta daga wasu kasashen musamman Amurka, wacce ta bayyana cewa Iran din ba zata ga shekaru 40 ba na nasara juyin.

Kamar yadda aka saba a kowace shekara dai, al'ummar kasar ta Iran, na gudanar jerin gwano domin nuna goyon baya ga tsarin da kasar take a kansa.

A nan birnin Tehran dubun dubatar jama'a ne ke haduwa a dandalin 'yanci na ''Azadi'', inda mahukuntan kasar ke jawabi. 

Kamar yadda kuma a sauran sassan kasar miliyoyin jama'a ke gudanar da irin wadannan taruka, tare da kara jaddada goyon bayansu ga juyin juya halin musuluncin.

Mirigayi Iman Khomeini, ya koma kasarsa a ranar 1 ga watan Fabrairu na shekara ta 1979, bayan shafe dogon lokaci na zaman hijira a birnin Paris na kasar Faransa.