Iran Ta Gabatar Da Wani Sabon Jirgin Yaki Na Karkashin Ruwa
(last modified Sun, 17 Feb 2019 19:10:36 GMT )
Feb 17, 2019 19:10 UTC
  •  Iran Ta Gabatar Da Wani Sabon Jirgin Yaki Na Karkashin Ruwa

Shugaban kasar Iran Dr Hassan ruhani ya yaye labulen fara amfani da wani sabon jirgin ruwan yaki na karkashin ruwa wato Submerrin mai suna Fateh a yau Lahadi a birnin Bandar Abbas na kudancin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv mai watsa shirye-shiryensa da harshen turanci a nan Tehran ta bayyana cewa sabon jirgin ruwan yakin yana iya cilla makamai masu linzami samfurin Cruise, sannan yana iya zuwa karkashin zuwa har zuwa zurfin mita 200. 

Banda haka jirgin ruwan yakin na karkashin ruwa yana da kayakin aiki na zamani, wadanda aka samar da su a cikin giga. Daga cikin na'urorin da jirgin yake da su sun hada da iya gani makiyi daga nesa yana da nauyin ton 527.

Daga yau Lahadi ne sojojin ruwa na kasar Iran zasu fara amfani da jirgin don tabbatar da tsaron kasa Iran da kuma ruwayen yankin.

Daga karshe labarin ya kammala da cewa kwararru daga cikin giuda ne suka kera jirgin ruwan, sannan dukkan sassansa 100/100 daga cikin gida aka samar da su.