Mar 11, 2019 10:32 UTC
  • Iran Ta Mika Sakon Ta'aziyya Ga Al'ummar Kasar Ethiopia

Gwamnatin kasar Iran ta mika sakon ta'aziyya ga al'ummar kasar Ethiopia dangane da hadarin da jirgin kasar kasar ya yi a jiya a birnin Addis Ababa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da ya fitar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran bahram Kasimi ya bayyana cewa, Iran tana mika sakon ta'aziyya da kuma alhini ga gwamnati da kuma al'ummar Ethiopia dangane da hadarin jirgin da ya faru, musamman ma ga iyalan wadanda suka rasa danginsu a sakamakon hadarin.

Kasimi ya ce ko shakka babu abin da ya faru abin bakin ciki matuka, musamman ma rasa rayukan jama'a da aka yi a wannan hadari.

A jiya ne wani jirgin fasinja na kamfanin Ethiopia Airlaine ya hadari jim kadan bayan tashinsa daga filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Addis Ababa, da nufin zuwa birnin nairobi na kasar Kenya, inda dukkanin mutanen 157 da ke cikin jirgin suka rasa rayukansu.

 

Tags