Mar 17, 2019 05:46 UTC
  • Iran Ta Bukaci A Gudanar da Zaman Gaggawa Na Kasashen Musulmi Kan batun Harin New Zealand

Gwamnatin kasar Iran ta bukaci da a gudanar da zaman gaggawa na kasashen musulmi kan batun harin da aka kaiwa musulmi a kasar New Zealand.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ne ya sanar da hakan bayan wata ganawa da suka yi da ministan harkokin wajen  kasar Turkiya Jawish Auglo kan batun, wanda kuma kasar Turkiya ce ke jagorancin na karba-karba na kungiyar kasashen musulmi.

Zarif ya ce abin da ya faru kan musulmi a  kasar New Zealand yana da daga hankali matuka, kuma ya zama wajibi akan kasashen musulmi su tattauna wannan batu, domin daukar matakan kare rayukan musulmi a kasashen da ba su da rinjaye, inda ake nuna musu wariya da kyama.

Yanzu haka dai jami’an tsaro  akasar at New Zealand sun kame mutumin day a kai hari da bindiga a kan musulmi a Christ Church, inda ya kashe musulmi 49 a cikin masallaci, tare da jikkata wasu fiye da 50.