Mar 21, 2019 05:41 UTC
  • Babban Hafsan Hafsoshi Sojin Kasar Iran Ya Tabbatar Da Ci Gaba Da Yaki Da Ta'addanci.

Yayin da yake ishara kan taron hadin gwiwa na kasashen Iran da Iraki da Siriya a birnin Damuscus, babban hafsan hafsoshin sojin jamhoriyar musulinci ta Iran janar Muhamad Bakiri ya ce kasashen uku sun cimma matsana na aiki tare a game da yaki da ta'addanci da nufin tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen.

An gudanar da wannan zama ne tsakanin manyan jami'an tsaron kasashen uku da suka hada da Janar Muhamad Bakiri babban hafsan hafsoshin sojin jamhoriyar musulinci ta Iran da Labtanar-janar Osman al-Ghanemi babban hafsan hafsoshin sojin kasar iraki da Imad Ali Abdullahi Ayyub ministan harakokin tsaron kasar Siriya a birnin Damuscus.

A gefen wannan zama babban hafsan hafsoshin sojin jamhoriyar musulinci ta Iran Janar Muhamad Bakiri a ranar talatar da ta gabata ya ziyarci yankunan da suka fuskanci mamayar 'yan ta'adda a baya, wato Deir-er-zor da Mayadin da Bu-kamal, inda ya gana da sojojin Siriya da kuma masu basu shawara kan harakokin tsaro na jamhoriyar musulinci ta Iran.

Alakar dake tsakanin buranan Tehran da Damuscus, alaka ce mai mahimancin gaske musaman ma a bangaren yaki da ta'addanci, dangane da mahimancin wannan alaka, yayin ziyarar da shugaba Asad na Siriya ya kawo birnin tehran kusan makuni uku da suka gabata, Jagoran juyin musulinci na kasar Iran Ayatollahi Aliyu Khamnei ya yi ishara kan tsayin daga da kuma kasancewa a bangaren al'ummar kasar Siriya tun da farko fara rikicin kasar, ya ce juriyar da al'ummar kasar Siriya suka yi a game da manyan kasashen Duniya Irinsu Amurka da Turai da kuma kawayensu na yankin, shakka babu sun samu nasara a yau.

Jagoran juyin musulinci ya ce nasarar da Sojojin Siriya gami da kungiyoyin gwagwarmaya na yankin suka samu ya yi sanadiyar fusatar mahukuntan Amurka tare da kuma wargaza duk wani shiri da suka yi a yankin, sannan ya kara da cewa sabon makircin da Amurka ke kulla da nufin ci gaba da zama a yankin musaman kan iyakokin kasashen Iraki da Siriya ba za su nasara ba, matukar dai kasashen uku suka ci gaba da aiki tare.

Shakka babu, kokarin da kasashen Iran da Siriya suka yi na yaki da ta'addanci a yankin babu wani makhluli da zai yi inkarinsa, kuma hakan zai ci gaba da kasancewa har sai lokacin da aka kawo karshen rikici da ta'addanci a yankin, kamar yadda kuma aka bayyana, kasantuwar mashawartar sojojin Iran Iran a kasar Siriya na zuwa ne bisa bukatar mahukuntan kasar ta Siriya, kuma yadda kuma mahukuntan na Siriya ke nanatawa, matukar dai Hukumomin siriya suka bukaci taimakon , Sojojin Iran din wajen yaki da ta'addanci, to shakka babu za su ci gaba da kasancewa a kasar.

A yayin da yake ishara kan wannan shekara ta 2019 da ya ce shekara ce ta samun babbar nasara a yankin, Abdul-Bari Atwan mai sharhi kan harakokin gabas ta tsakiya ya ce a hakikanin gaskiya duk masu adawa da fitar Sojojin Amurka, na kokarin kare manufofin haramtacciyar kasar Irsa'il ne da tsaronta, ba wai nufin yaki da ta'addanci ko kare manufofin kasar Amurka a yankin gabas ta tsakiya ba.

Yayin da yake bayyana mahimanci wannan zama, Shugaba Bashar Al-asad ya tabbatar da cewa: wannan taro na nuni da cewa a fagen yaki da makiya wadannan kasashen guda uku, manufarsu daya wanda shi ne yaki da ta'adda.

A nasa bangare, babban hafsan hafsoshin sojin Iran ya ce yaki da ta'addanci da kuma kare kasar Siriya, yana nufin kare kasashen Iran da Iraki, domin 'yan ta'adda hadari ne ga dukkanin kasashen uku da ma yankin baki daya, don haka kamata al'ummar yanki suka zage damtse domin kawo  kakkabe 'yan ta'addar daga yankin gaba daya.