Jawabin Rauhani a wajen taron kungiyar hadin kan kasashen Musulmi OCI
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa karfafa alaka da kasashen musulmi shine muhimin abu da Jumhoriyar musulinci ta sanya a gaba
A yayin jawabin da ya gabatar a taron kungiyar hadin kai na kasashen musulmi OCI dake gudana a birnin Estambul na kasar Turkiya a yau Alkamis, Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya bayyana cewa A yau dukkanin manbobin wannan kungiya mun taru a nan birnin Estanbul domin murya guda daya, hada kai domin tabbatar da adalci gami da sulhu,kuma wannan babbar dama da ya kamata mu yi amfani da ita domin yin tunani kan halin da musulmi ke ciki a Duniya.
Shugaban Iran ya tabbatar da cewa dukkanin yunkuri na kokarin raba kawunan manbobin kungiyar ba shi da wani tasiri a wajen mu, kuma sabani ko rashin jutuwar dake tsakanin wasu kasashen musulmi abu ne da za a iya magance shi ta hanyar Diplomasiya.
Yayin da yake ishara kan bullar kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi da kuma babbancin ra'ayi a tsakanin mazhabobin Musulinci, Dakta Hasan Rauhani ya bayyana cewa tun lokacin da musulinci ya bunkasa yake fuskantar jajjayar da ba ta da wani amfani, kuma hakan ya sharewa makiya fage daga waje wajen su ci gaba da yakar sa.
Shugaban kasar Iran ya bayyana bakin cikinsa kan yadda wasu kasashe ke taimakawa wasu kungiyoyin masu adawa da musulinci kudade domin kawai a gogawa musulinci kashin kaji, tare da bayyana shi a matsayin ta'addanci, don haka wajibi ne kasashen musulmi su hada kai domin tabbatar da sulhu tare da tunkarar wannan ta'addanci da hakan zai sanya a medo da tsaro a duniyar musulinci.
Dakta Hasan Rauhani ya kara da cewa Haramcecciyar kasar isra'ila ita ce ta samar da wannan ta'addanci a Duniya, kuma abinda zai tabbatar da hakan shi ne a ko wata rana yadda Sojojin hKI ke ci gaba da kisan gilla kan Al'ummar Palastinawa, babban abin bakin ciki a nan kuma shine yadda Duniya ta ci gaba da yin shuru a kan wannan batu.
Shugaba Rauhani ya tabbatar da cewa Jumhoriyr musulinci ta Iran za ta kasance tare da kuma goyon bayan dukkanin kasashen musulmi domin tunkarar duk wani fice gona da iri, barazana, mamaya da kuma ta'addanci.