Tawagar Iran Ta Kaurace Wa Zaman OIC A Istanbul
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i3922-tawagar_iran_ta_kaurace_wa_zaman_oic_a_istanbul
Tawagar Iran ta kaurace wa zaman rufe taron kungiyar kasashen musulmi (OIC) a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 15, 2016 11:09 UTC
  • Tawagar Iran Ta Kaurace Wa Zaman OIC A Istanbul

Tawagar Iran ta kaurace wa zaman rufe taron kungiyar kasashen musulmi (OIC) a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

A rahoton da tashar talabijin ta PressTV ta bayar daga birnin Istanbul na kasar Turkiya, shugaga Rauhani na Iran tare da tawagarsa sun kaurace wa halartar zaman taron karshen saboda abin da suka kira babban tasirin da Isra'ila ta samu na kutsawa a cikin kudirorin taron ta hanyar wasu masu wakiltarta a wurin.

A cikin bayanin bayan taron wanda aka raba wa mahalarta taron, an bayyana Iran a matsayin mai mara baya ga 'yan ta'adda a cikin kasashe mambobi a kungiyar, musamman a Syria da Yemen, daga cikin kungiyoyin da take mara wa baya kuwa har da kungiyar Hizbullah ta Lebanon, wadda bayanin ya bayyana ta a matsayin wadda ta hana ruwa gudu a Syria.

Bisa ga al'ada dai a kan zanta da sauran kasashe mambobi na kungiyar ta OIC domin yin shawara kan bayanin karshen taro da za a fitar, amma a wannan karon sai dai aka rarraba musu bayanin a rubuce bayan da wakilan Saudiyya tare da babban sakatren kungiyar gami da wasu 'yan tsirarun kasashe suka rubuta bayanin ta bayan fage, saboda masaniyar da da suke da ita kan cewa wasu daga cikin kasash ba za su taba aminta da abin da aka rubuta ba.

Tun kafin wannan lokacin dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Abbas Araghchi ya bayyana cewa, babban abin takaici yadda Isra'ila ta zama mai fada a ji tare da zartar da kudurorinta acikin kungiyar OIC ta hanyar wasu kasashe da wakiltarta a cikin kungiyar, wadanda kuma su ne suka kankane komai a cikin wannan kungiya.